![]() |
Mali/Nijar/Burikina Faso |
Kasashen kungiyar AES sun janye jakadunsu daga kasar Aljeriya, bayan zargin da kasar Mali ta yi cewa Aljeriya ta harbo mata jirgin yaki marar matuki a ranar 31 ga Maris zuwa safiyar 1 ga Afrilu.
A cewar sanarwar da gwamnatin Mali ta fitar, an harbo jirgin mai kirar TZ-98D a yankin Tin-Zaouatène da ke jihar Kidal, kusa da iyakar Aljeriya.
Gwamnatin Mali ta zargi Aljeriya da keta huruminta da kuma amfani da makami mai linzami wajen kakkabo jirgin.
Sai dai daga bisani, Aljeriya ta bayyana a kafafen yada labaranta cewa ta kakkabo wani jirgi da ya shige sararinta da kusan kilomita biyu, zargin da Mali ta musanta.