![]() |
Peter Obi |
Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, ya jinjinawa rundunar ’yan sandan Najeriya bisa janye gayyatar da ta yi wa Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II, dangane da wani bincike kan zargin mutuwar wani yayin bukukuwan Sallah.
Obi ya bayyana cewa tun da farko, bai kamata a aikata hakan ba, la’akari da yanayin da ake ciki a jihar.
A cewarsa, hakan na iya kara dagula lamarin da ke bukatar kulawa ta musamman kamar yadda jaridar PUNCH ta sanar.