![]() |
Nuhu Ribadu |
Mai bai awa shugaban Nijeriya shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu ya bayyana cewa Nijeriya ta samu ci gaba sama da kashi 90 cikin 100 akan rashin tsaro a gwamnatin shugaba Bola Tinubu.
Ribadu ya bayyana haka ne a garin Jos na jihar Filato a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan wata ganawa da kwamandan rundunar ‘Operation Safe Haven’ Manjo Janar Folusho Oyinlola a ofishinsa, biyo bayan harin da ‘yan bindiga suka kai kan al’ummar Bokkos wanda ya yi sanadin mutuwar mazauna garin.
A cewarsa, gwamnatin shugaba Tinubu ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasar nan.
Ya ce cikin shekaru 2 da suka wuce, an samu ragin yawan mace-mace da tashin hankali da kusan kashi 90 cikin 100 a kasar.
Wallahi akwai Rina akaba sosai