Ma’aikatar Harkokin Wajen Sudan ta bayyana rashin amincewarta da kuma kauracewa wani babban taro da Birtaniya ke shirin gudanarwa a tsakiyar watan Afrilu a birnin London, wanda zai tattauna rikicin Sudan.
A cikin wata wasika da ya aikewa Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya, David Lammy, Ministan Harkokin Wajen Sudan, Ali Yousif, ya soki matakin Birtaniya na gayyatar wasu kasashe kamar UAE, Chadi da Kenya, wadanda Sudan ke zargi da marawa dakarun Rapid Support Forces (RSF) baya.
Taron dai na gudana ne tare da hadin gwiwar Tarayyar Turai (EU), Faransa, da Jamus, da nufin lalubo mafita kan rikicin da ya dabaibaye kasar Sudan.