![]() |
Victoria/Kashim Shettima |
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya gana da Gimbiya Victoria, magajiyar sarautar kasar Sweden, wadda ke ziyarar aiki ta kwanaki uku a Nijeriya.
Ziyarar Gimbiyar na daga cikin matakan da ake dauka domin karfafa dangantakar diflomasiyya da tattalin arziki tsakanin Nijeriya da Sweden.
A yayin taron, Shettima ya bayyana cewa Nijeriya za ta ci gaba da kasancewa abokiyar kut da kut da Sweden, inda ya kara da cewa wannan ziyara za ta bude sabon babi na karfafa alaka tsakanin hukumomin kasashen biyu da kuma bunkasa musayar al’adu.