![]() |
Majalisar wakilai |
Majalisar Wakilai ta amince da kudurin da ke neman kayyade shekarun masu neman kujerar shugaban kasa da na gwamna zuwa karancin shekaru 60, yayin da kudirin ya tsallake karatu na biyu a zauren majalisar.
Kudurin wanda dan majalisa Ikeagwuonu Ugochinyere, mai wakiltar mazabar Ideato ta Arewa daga jihar Imo, ya gabatar, yana neman a gyara sashe na 131 da na 179 na kundin tsarin mulkin Nijeriya.
A cewar Ugochinyere, ya kamata a sabunta tsarin ne domin bai wa sabbin jini damar shiga tafiyar siyasa, tare da tabbatar da cewa wadanda ke rike da manyan mukamai na kasa suna da kuzari da sabbin dabaru.
Yanzu haka, kudurin na jiran ci gaba da tattaunawa da nazari a matakai na gaba kafin ya kai ga zama doka.