![]() |
Natasha Akpoti |
Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta maka Sanata Onyekachi Nwebonyi a kotu tana neman diyya naira biliyan biyar bisa zargin bata suna da zarge-zargen da ke barazana ga martabarta.
Kotu ta karɓi karar ne bayan Sanata Nwebonyi ya yi wasu kalamai a taron manema labarai da Natasha ke zargin an taba kimarta a zarge- zarge marasa tushe, waɗanda suka shafi mutuncinta da rayuwarta ta siyasa.
Lauyan Sanata Natasha Michael Jonathan Numa, da ya shigar da karar, mai lamba Suit No: W/1359:25 a babbar kotun birnin tarayya Abuja ya ce kalaman sun janyo mata tozarta a idon jama’a kuma suna iya gurgunta aikinta a majalisa.
Sanata Nwebonyi bai mayar da martani ba tukuna, amma ana sa ran kotu za ta fara sauraron shari’ar nan ba da jimawa ba.