![]() |
Bola Ahmad Tinubu |
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnati za ta tabbatar da cewa albashin ’yan sanda ya dace da hadurran da suke fuskanta a aikin yau da kullum.
Tinubu, ta bakin mataimakinsa Kashim Shettima a bikin makon ’yan sanda, ya ce ana kokarin inganta walwalar jami’an tsaro domin kara musu kwarin gwiwa.
Ya kuma jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin gwamnati da jami’an tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya.