Sudan ta Kudu ta bayyana rashin jin daɗinta kan matakin da gwamnatin Amurka ta dauka na janye biza ga dukkan ’yan ƙasar, tana mai cewa hakan ba gaskiya ba ne kuma ya samo asali ne daga kuskuren tantance ɗan wata ƙasa.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya sanar da wannan mataki bisa zargin cewa Sudan ta Kudu ta ki karɓar ’yan ƙasarta da aka kora daga Amurka.
Sai dai Ma’aikatar Harkokin Wajen Sudan ta Kudu ta ce batun ya danganci wani ɗan ƙasar Kongo da aka dauka a matsayin ɗan Sudan ta Kudu, wanda yanzu haka aka mayar da shi Amurka don sake duba lamarin.
Wannan shi ne karon farko tun dawowar Shugaba Donald Trump kan mulki da Amurka ke kakabawa wata ƙasa takunkumin hana biza ga duk masu fasfo dinta.