Wasu daga cikin ‘yan kwamitin gudanarwa na hukumar kula da aikin hajji ta Nijeriya sun kai karar shugaban hukumar ga ofishin mataimakin shugaban kasa.
Mambobin kwamitin na zargin shugabban NAHCON Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan da watsi da su a shirye-shiryen aikin hajjin 2025.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mambobin kwamitin gudanarwa na NAHCON da suka rattaba hannu a takardar korafin sun hada da Professor Muhammad Umaru Ndagi da Alhaji Abba K. Jato da Shaykh Muhammad Bn Uthman da Hajiya Aishat Obi da Hajiya Zainab Musa da kuma Dr Tajudeen Abefe Oladejo, sai Professor Adedimeji Mahfouz Adebola tare da Professor Musa Inuwa Fodio
Mambobin sun yi zargin cewa shugabancin hukumar NAHCON bai tuntube su ba a wajen tsayar da farashin kudin kujerar hajjin bana da kuma wajen zabar kamfanonin da za su yi alhazai hidima a hajjin na bana.
Kawo yanzu hukumar ta NAHCON ba ta ce komai ba a kan wannan zargin, sai dai a wata hira da DCL Hausa a kwanakin baya, shugaban hukumar Farfesa Pakistan ya ce babu wani abu da suke yi da ya saba wa doka, yana mai jaddada cewa shugabancinsa walwalar alhazai ya sanya a gaba.