A cikin sanarwar da ofishin cinikayya na kasar Amurka ya fitar, an yi gargadin cewa wannan mataki yana zama babban kalubale ga masu fitar da kaya daga Amurka, tare da toshe hanya ga kasuwancin kayayyaki daga Amurka zuwa Nijeriya, wanda shi ne daya daga cikin manyan kasuwanni a Afirka.
Korafin daga Amurka yana zuwa bayan sanarwar Shugaba Donald Trump na karin haraji ga kayayyakin China, yayin da kuma ya sanya sabbin haraji na kashi 14% kan kayayyakin Naira biliyan 323.96 da ake fitarwa daga Nijeriya, wanda hakan ke barazana ga fitar da kayayyakin Nijeriya ba tare da mai ba zuwa kasuwar Amurka.
Amurka ta yi kira ga Nijeriya da ta duba wannan mataki da kyau, domin gujewa tasirin da zai iya yi wa kasuwancin kasashen biyu.