Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya bukaci ’yan Najeriya da su daina biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutane, yana mai cewa hakan na kara karfafa ayyukan ’yan ta’adda a fadin kasar.
Ribadu ya bayyana hakan ne a yayin da yake karbar wasu mutane 60 da aka ceto daga hannun masu garkuwa da mutane a karamar hukumar Zangon Kataf, Jihar Kaduna. Wadanda aka sace din an kubutar da su ne bayan wani samame da jami’an tsaro suka kai sansanin ’yan ta’addan a yankin.
A cewarsa, biyan kudin fansa na taimaka wa masu aikata laifin wajen ci gaba da wannan mummunar sana’a, yana mai kira ga al’umma da su hada kai da hukumomin tsaro domin kawar da matsalar gaba daya.
Ya kuma yaba da kokarin da dakarun soji da sauran jami’an tsaro ke yi wajen yaki da ayyukan garkuwa da mutane da sauran kalubalen tsaro a fadin kasar.