Majalisar Zartarwa ta Najeriya ta amince da ci gaba da sayar da danyen mai a cikin gida da kudin Naira, cikin wani mataki da tace zai taimaka wajen inganta tattalin arzikin kasar.
Wannan shawara ta zo ne bayan tattaunawa tsakanin manyan jami’an gwamnati da kuma masu ruwa da tsaki a fannin man fetur a zaman majalisar na wannan mako.
Ana hasashen wannan tsarin zai inganta harkokin kasuwancin man fetur a cikin gida, tare da rage dogaro da kasashen waje wajen siyo danyen mai.
Shawarar ta samu goyon bayan manyan ministoci a taron Majalisar Zartarwa, wanda ya kara bayyana kudurin gwamnatin Najeriya na inganta tsaro da kuma bunkasa masana’antar mai.