Dan takarar shugaban kasa na Labour Party a zaben 2023, ya ce talaucin da ake fama da shi a Nijeriya ya makura, ta yadda wadanda ke ba shi abubuwa a baya yanzu rokonsa suke ya taimaka musu.
Da yake magana a taron kwamitin zartarwa na kasa da kuma taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyarsa a Abuja, Obi ya ce lokaci ya yi na ceton Najeriya.
Ya kara da cewa a bayyane take al’amura na tafiya ba daidai ba kuma Najeriya na rugujewa, mutane suna kara fadawa cikin talauci a kowace rana.