Ra’ayin gwamnatin tarayya da Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya banbanta game da yawaitar hare-hare a jihar.
Gwamnan ya yi ikirarin cewa ‘yan ta’adda na samun galaba a jihar, inda ya ba da misali da hare-haren da aka kai a sansanin sojoji da kuma satar mutane.
Amma ninistan yada labarai da wayar da kan jama’a Mohammed Idris, ya ce jami’an tsaro na aiki ba dare ba rana domin ganin an shawo kan matsalar a sassan jihar Borno.