![]() |
Amimu Ibrahim Kasuwar Daji |
Rahotanni sun bayyana cewa dan majalisar ya rasu ne da sanyin safiyar Laraba.
Jam’iyyar APC a jihar Zamfara, ta bayyana alhinin rasuwar dan majalisar.
A wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar a jihar Zamfara Yusuf Idris ya fitar, kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na jihar, shuwagabannin jam’iyyar, da magoya bayansa sun yi jimamin rashinsa, inda ya bayyana Hon. Ibrahim Kasuwar-Daji a matsayin mutum mai kwazo, da gaskiya, kuma mai tsoron Allah, wanda ya yi aiki a mazabarsa sossai.
Jam’iyyar ta mika ta’aziyyarta ga iyalan marigayin, al’ummar Kaura Namoda ta Kudu, da ‘yan majalisar dokokin jihar, inda ta yi addu’ar Allah ya ba shi Jannatul Firdaus.