Nijeriya ita ce ta kasa ta 13 a duniya, da ‘yan kasarta ke sayen man fetur da sauki, kuma ta daya a cikin kasashen yammacin Afrika, a cewar rahoton globalpetrolprices.
Rahoton ya nuna cewa har yanzu farashin litar man fetur a Nijeriya bai kai dala daya ba, idan aka sauya Naira zuwa kudin dala, kasancewar ana sayar da fetur din ne daga Naira 940.
Jaridar Punch ta ambato rahoton na cewa fetur a Nijeriya yana kan dala 0.6 ne kowace lita a halin yanzu, sai kasar Laberiya, da farashin man fetur ya kai dala $0.87, kwatankwacin Naira 1,365. inda a kasar Ghana ake sayar da lita daya kan N1611.
Jamhuriyar Benin ana sayar da man fetur kusan Naira 1,817 kan kowace lita, yayin da na Togo ke biyan Naira 1,778.
Sai kasar Cape Verde da ya kai N2,089 kowace lita, a Guinea kuwa ake sayar da fetur din N2,170.
A Burkina Faso ana sayar da man fetur kan Naira 2,223. N2,172 a kasar Saliyo, a Ivory Coast kuwa N2,172, yayin da Senegal ake sayar da fetur N2,589, can kuwa a kasar Mali ake sayar da shi N2,235.
A jerin kasashen da fetur ya fi sauki a duniya, kasar Libya ita ce ta farko, inda ake sayar da kowace lita kan Naira 42, sai kasar Iran a kan N45 sai Venezuela a kan N54.
A Angola N512, a Masar N518, da Kuwait N533.
Kasar Hong Kong ce ke kan gaba a kasashen da ake sayar da fetur da tsada, inda farashin ya kai Naira 5,410 kan kowace lita. Sai Iceland ta biya N3,655, Denmark ta biya N3,375, Netherlands ana sayarwa N3,268, sai kuma kasar Isra’ila a kan N3,128.
A cewar rahoton, a bayyana take duk kasashe masu karfin tattalin arziki, to farashin man fetur ya fi tsada a can, yayin da kasashe masu fama da talauci da kuma kasashen da ke hako mai da kuma fitar da man fetur suke da rahusa sosai.