![]() |
Nasir Idris |
Ruwan sama kamar da bakin kwarya a jihar Kebbi ya lalata gidaje da dama a karamar hukumar Shanga ta jihar.
Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa mamakon ruwan ya yi sanadiyyar rugujewar gidaje masu tarin yawa a Garin Kestu na mazabar Atuwo a karamar hukumar Shanga ta jihar Kebbi, tare Kuma da haddasa asarar dukiya ta miliyoyin Naira a yankin
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris ya jajanta wa al’ummar Garin Kestu da ke unguwar Atuwo a karamar hukumar Shanga, tare da alkawarin tallafawa wadanda abin ya shafa.
Kamar yadda wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan Ahmed Idris ya fitar, ta bayyana.