Matatar man Dangote ta sanar da rage farashin man fetur da ake sayarwa ga ‘yan kasuwa zuwa N856 kowace lita, wanda ya samu ragin naira 15 daga farashin N865 da ake sayarwa a baya.
Sabon farashin, wanda aka fara aiwatarwa a ranar Laraba, an sanar da shi ga abokan huldar matatar ta Dangote a wata sanarwa da ta aike a safiyar ranar Alhamis.
Jaridar Punch ta gano cewa tuni sabon farashin fetur na N865 ga kowace lita ya fara aiki a gidajen mai.