Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF) ta yi Allah-wadai da ’yan siyasa da ke fara yakin neman zabe na shekarar 2027, inda ta bukaci su mayar da hankali wajen magance matsalolin da ke addabar kasar nan maimakon fara yakin neman zabe a yanzu.
A yayin taron kwamitin zartaswa na kasa a Kaduna ranar Alhamis, shugaban ACF, Mamman Osuman, ya bayyana cewa ya kamata shugabannin kasar su maida hankali kan harkokin mulki da za su magance matsalolin da ‘yan Najeriya ke fuskanta, musamman a wannan lokaci, maimakon shigar da kai cikin harkokin siyasa.
Osuman ya kuma bayyana damuwarsa kan rashin rayuka a jihohin Filato, Edo, da Borno, da rikicin da ke gudana tsakanin Kogi da Enugu, musamman kan yankin Ette Community. Haka zalika, ya jaddada cewa matsalolin tattalin arziki da suka hada da tsadar rayuwa, kayayyaki, da sufuri suna daga cikin muhimman batutuwan da shugabanni ya kamata su mayar da hankali.