Jami’an sashin yaki da masu garkuwa da mutane na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, tare da hadin gwiwar ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, sun ceto mutane 17 da aka yi garkuwa da su a ranar 3 ga Maris, 2025, daga Sarkin Pawa, jihar Neja.
Rundunar ‘yan sandan ta bayyana cewa wannan nasara na daga cikin kokarin Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun, wanda ya jagoranci jami’an leken asiri da sauran hukumomin tsaro domin magance matsalolin tsaro. A cewar rundunar, an samu bindigogi kirar AK-47 guda 21 a sansanin masu garkuwar da aka kame.
Daga cikin wadanda aka ceto sun hada da Williams Ubadia, Samuel Ezekiel, Ishaku Ishaya, Rebecca Ezekiel, da Victoria Ishaya, da sauran su. Dukkanin mutanen da aka ceto an kai su asibitin ‘yan sanda da ke Kaduna domin duba lafiyarsu, kuma an tabbatar da cewa suna cikin koshin lafiya.