A cikin wata sanarwa da Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (OSGF) ya fitar, gwamnatin ta ce tana bin tanadin kundin tsarin mulkin kasa na shekarar 1999 (wanda aka yi wa kwanskwarima) musamman sashen 14, wajen tabbatar da adalci da wakilci daga dukkan yankuna.
Sanarwar ta ce Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, na da cikakken burin hadin kan kasa, kuma yana yin nade-nade ne bisa tushen gaskiya, adalci da ga kowa da kowa.
Ofishin sakataren gwamnatin ya bukaci jama’a da su yi watsi da jita-jitar da ba su da tushe, tare da shawartar su da su dinga dogaro da hanyoyin sadarwa na hukuma wajen samun sahihan bayanai.
A karshe, sanarwar ta gargadi masu yada kalaman rarrabuwar kai da zargin da ba su da tabbas da su daina, domin hakan ba zai amfani kasar nan ba.