Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Olabode George, ya gargadi shugaban riko na jihar Ribas, Admiral Ibok-Ete Ibas mai ritaya, kan nade-naden da yake yi a kwanan nan da kuma sake fasalin hukumomin jihar.
Bode George ya bayyana hakan a matsayin abinda ya saba doka da kuma yiwuwar yin da na sani a gaba.
Ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar da aya fitar yau Jumu’a, inda ya bukaci Ibas da ya mutunta kundin tsarin mulki da bin doka da oda.
Jigon na PDP ya kuma yi soka kan shugabannin rikon kwarya na kananan hukumomi 23 da ya naɗa, duk kuwa da umarnin da kotu ta bayar na haramta irin wadannan ayyuka.