Gwamnatin tarayya ta yi hasashen za a tafka mamakon ruwan sama da ambaliya a jihohi 30 da kuma babban birnin tarayya Abuja.
Jihohin da za su fuskanci ambaliyar ruwa sun hada da Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Borno, Cross-River, Delta, Ebonyi, Edo, Gombe, Imo, Jigawa, Kebbi, Kogi, Kwara, Lagos, Nasarawa, Niger, Ogun, Ondo, Osun, Oyo, Rivers, Sokoto, Taraba, Yobe, Zamfara da kuma babban birnin tarayya.
Ministan albarkatun ruwa da tsaftar mahalli, Joseph Utsev, ya ce za a fuskanci ambaliyar ruwa a yankunan da ke gabar teku da koguna a wasu sassan yankin kudu maso kudancin kasar.