Madugun adawar siyasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana cewa ziyarar da ya kai wa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a Kaduna ba ta da alaka da wata tattaunawa ko hadakar siyasa da ke da nasaba da zaben 2027.
Atiku, wanda ya jagoranci wasu fitattun ’yan siyasa ciki har da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai da tsohon gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal, ya ce sun kai wa Buhari ziyara ne domin gaisuwar Sallah da sada zumunci. Ya kara da cewa, bayan ya kammala ayyukansa na Sallah a Adamawa, ya samu zarafin kai wa tsohon shugaban kasar ziyara.
Ziyarar na zuwa ne kwanaki biyu bayan gwamnonin jam’iyyar APC karkashin jagorancin Sanata Hope Uzodimma su ma suka kai irin wannan ziyarar gaisuwa ga Buhari. Wannan ya kara janyo ce-ce-ku-ce a fagen siyasa musamman kan makomar zabubbuka masu zuwa, amma Atiku ya jaddada cewa tafiyarsu ba siyasa ba ce.