Jami’an rundunar ‘yan sanda a Jihar Bauchi sun sanar da kame Umar Sule, mai shekaru 54, bisa zargin yin lalata da diyar cikinsa, budurwa mai kimanin shekaru 17 da haihuwa har ta samu ciki.
Kakakin hukumar, Ahmed Wakil, cikin sanarwar da ya fitar, ya ce sun samu korafi daga Abdullahi Baban Karatu, mai shekaru 55, daga kauyen Kurmin Ado, kan zargin da ake yi wa Sule na aikata laifin tare da diyarsa a lokuta daban-daban, wanda ya sabbaba ta dauki ciki na watanni uku, bisa ga rahoton likita.”
Sanarwar ta kara da cewa, kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Sani-Omolori Aliyu, ya umarci a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.