![]() |
Amorim/Onana |
Mai tsaron ragar Manchester United, André Onana, ba ya cikin jerin ‘yan wasan da za su buga wasan Premier da Newcastle United a Lahadin nan.
A cewar rahotanni daga kwararre a harkar kwallon kafa Fabrizio Romano, kocin kungiyar Rúben Amorim ya sanar da Onana hukuncin da ya dauka bayan wasan da United ta buga da Olympique Lyon na UEFA Europa League.
Kocin ya shawarci Onana da ya yi ɗan hutu daga wasan ƙwallon ƙafa don samun kuzari.
An rawaito cewa a makon da muke ban kwana da shi Onana ya yi wasu kura-kurai a lokacin da kungiyarsa ta buga wasa da Olympique Lyon wanda hakan ya ba su matsala a wasan.