Tsohon shugaban Nijeriya Cif Olusegun Obasanjo ya ce ‘yan Nijeriya ba su da wata hujja ta zama matalauta duba da yalwar albarkatun da Allah Ya huwace wa kasar.
Olusegun Obasanjo ya ce Nijeriya na da albarkatun kasa sosai, amma tana fama da matsalar rashin kyakkyawan amfani da su yadda ya kamata da hakan ya kakaba talaucin babu gaira babu dalilin a tsakanin ‘yan kasar.