![]() |
Bola Ahmad Timubu |
Wata kotu a Amurka ta umurci manyan jami’an tsaron kasar da su fitar da bayanan sirri da aka samu kan Shugaba Bola Tinubu a lokacin wani binciken da gwamnatin ta yi a shekarun 1990.
Alkalin kotun, Beryl Howell, ya ba da umarnin ne, yana mai cewa rufe bayanan ba’a bayyana wa jama’a ba, ba abu ne mai ma’ana ba.
Ba’amurke, Aaron Greenspan ne, ya shigar da kara a watan Yunin 2023 a karkashin dokar ‘yancin fitar da bayanai (FOIA) ofishin zartarwa na lauyoyin Amurka, ma’aikatar bincike ta (FBI),hukumar kula da magunguna (DEA), da hukumar leken asiri ta (CIA).
A cikin korafin nasa, Greenspan ya zargi hukumomin tsaro da karya dokar FOIA ta hanyar gaza fitar da bayanan cikin lokacin da aka kayyade, takardun da suka shafi binciken kan Shugaba Tinubu da wani Abiodun Agbele.
Agskiya bola tunubu bamutumin kirki bane saboda baya tausayawa masu rauni daga cikin bayun Allah Wanda yakeci da haqqinsu.
Muna rokon Allah ya kwacemu daga hannu wannan Azzalumi.
Ameen