Fitaccen lauya mai rajin kare hakkin dan’adam, Femi Falana, SAN, ya shawarci matasan Nijeriya da su karbo kasar daga hannun dattijai ta dawo hannunsu.
Dan gwagwarmaya Falana ya bayar da wannan shawara ne a birnin Legas, yayin taron shekara-shekara karo na shida na jagorancin matasa, wanda aka lakaba wa suna ‘Resilience, Innovation, Social Responsibility and Entrepreneurship (RISE 2025).
Falana ya ce abubuwa ba su kasance kamar yadda suke a da ba, saboda haka ya zama wajibi matasa su kwato kasarsu kuma su sake fasalta ta yadda ya kamata.
Ya kara da cewa matasa suna shan wahala sakamakon halin da kasar ta shiga, saboda haka akwai bukatar matasa su tashi tsaye don zage damtse su yi abin da ya kamata.