Fursunonin da ke gidajen gyaran hali daban-daban a fadin Nijeriya sun yi zargin cewa ba a inganta abincinsu yadda ya kamata.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Nijeriya da kwamitin mai zaman kansa da ministan harkokin cikin gida Olubunmi Tunji -Ojo ya kafa a watan Satumbar da ya gabata domin binciken zargin cin hanci da rashawa.