Daniel Bwala, mai ba shugaban kasa Bola Tinubu shawara ta musamman kan harkokin siyasa, ya ce ya kamata jam’iyyar APC ta yi hattara da Sanatan Borno ta Kudu, Ali Ndume, yana mai zargin cewa lissafin dan majalisar da ruhinsa a siyasa sun bar jam’iyyar.
Bwala ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da gidan talabijin na Channels, inda yake jan hankalin jam’iyyar APC musamman shugaban jam’iyyar, Abdullahi Ganduje, cewa Sanatan na a cikin jam’iyyar, amma ruhinsa na wani waje na daban.
Inda ya kara da cewa kamata ya yi Ndume ya fice daga jam’iyyar kai tsaye kamar yadda Nasiru El-Rufai ya yi.