Hukumar kula da gidajen gyaran ta Nijeriya, ta yi watsi da rahotannin da ke cewa ana barin fursunonin da yunwa a cibiyoyin da ake tsare da su a fadin kasar.
Da yake mayar da martani kan labarin da ake yadawa, jami’in hulda da jama’a na hukumar Abubakar Umar, ya ce labarin sam ba gaskiya ba ne, kuma ba ya nuna ainihin halin da ‘yan gidan yarin suke ciki.
A cewarsa, dukkanin cibiyoyin da ake tsare da mutanen ana tabbatar da ciyar da duk fursunonin cikin lokaci kuma yadda ya kamata.