Jami’an hukumar tattara haraji ta jihar Kano sun rufe wuraren kasuwanci na wasu kamfanoni tara bisa zargin kin biyan kudaden haraji.
Daga cikin wuraren da aka rufe har da makarantu da wasu wuraren kasuwanci yayin zagayen rufe wuraren da tawagar KIRS ta gudanar.
A cewar jagoran tawagar jami’an hukumar Abbas Sa’idu, matakin da hukumar ta dauka ya zama dole domin kamfanonin sun kasa amsa wasikun da hukumar ta aika musu, tare da sanar da su kan bukatar biyan kudaden harajin da ake bin su.