Wani sabon rahoto da hukumar kididdiga ta Nijeriya ta fitar ya nuna cewa kididdigar hauhawar farashin kayayyaki ta karu zuwa kashi 24.23 a watan Maris na 2025, daga kashi 23.18 cikin 100 da aka samu a watan Fabrairu.
Adadin ya nuna karuwar kashi 1.05 cikin dari, wanda ke nuna ci gaba tashin farashin kaya a kowance matakin a fadin kasar.
A kididdigar wata wata, hauhawar farashin kayayyaki ya karu ne da kashi 3.90 cikin 100 a cikin Maris, idan aka kwatanta da kashi 2.04 cikin 100 a watan Fabrairu, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.