A wani rahoto da gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa ragin ya nuna an samu raguwar wutar lantarki da kashi 42 cikin dari ga kasar.
Ministan makamashi na Nijar, Haoua Amadou, ya ce matakin ya sa wutar lantarkin kasar ta ragu da kashi 30 zuwa 50 cikin 100, kuma ya tilasta wa kamfanin samar da wutar lantarki mallakar gwamnati Nigelec aiwatar da shirin rage wutar lantarki da ka iya daukar kwanaki da dama, musamman a birnin Yamai.
Nijeriya ta dakatar da fitar da wutar lantarkin da take fitarwa zuwa yankin yammacin Afirka a wani bangare na takunkumin da yankin ya kakaba wa gwamnatin mulkin soji da ta hambarar da shugaba Mohamed Bazoum a watan Yulin 2023.