Gwamnatin jihar Zamfara ta biya bashin Naira biliyan 1 da kamfanin rarraba wutar lantarki na Kaduna,KEDCO ke bi.
Gwamnatin ta kuma kara wa’adin sabuwar hukumar samar da wutar lantarki ta jihar Zamfara, ZEA, da inganta samar da wutar lantarki ga al’ummomin da ke jihar.
Babban sakataren hukumar ZEA, Muzammil Idris ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN a Gusau, ranar Alhamis.
Idris ya ce gwamnatin Dauda Lawal ta kubutar da jihar daga basussukan da ke zama cikas ga ci gaban da ake sa ran za a samu na ayyukan gwamnati domin ci gaban tattalin arzikin jihar.
A cewarsa, tuni hukumar ta yi tsarin aiki na shekaru 10 da dabarun aiwatarwa domin samun samun sauki ga al’ummar jihar.