Fadar shugaban Nijeriya ta mayar da martani kan sukar da ake yi wa Shugaba Tinubu, yayin da yake ci gaba da zama a kasar waje a dai dai lokacin da kasar ke fuskantar kalubale da dama.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Bayo Onanuga ya fitar, ya ce shugaban yana ci gaba da gudanar cikin harkokin mulkin Najeriya duk da cewa yana Turai, kuma yana sa ido sosai kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya.
Ya kara da cewa shugaban zai dawo Abuja domin ci gaba da aikinsa bayan hutun Esther.
Duk da cewa fadar shugaban kasa ta ce shugaba Tinubu na ziyarar aiki ne a kasar a hukumance, sai dai rahotanni sun ce ya gana da mai bai wa Trump shawara kan harkokin tattalin arziki da tsaro.