Ministan babban birnin Abuja Nyesom Wike, ya bayyana cewa jam’iyyar PDP ba ta shirya cin zaben 2027 ba, kuma ba ta da wani kyakkyawan tsari da za ta iya kayar da jam’iyyar APC.
Ministan ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai a Abuja.
Wike ya ce halin rashin tabbas da PDP ke ciki, su kan su jagororin sun san ba da gaske suke ba, don haka ba su shirya tunkarar 2027 ba.