Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya yi watsi da gamayyar jam’iyyun adawa na siyasa da ake tattaunawa a kai, da nufin kifar da Gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu da jam’iyyar APC a 2027, yana mai bayyana hakan a matsayin bata lokaci.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, wanda ya kasance dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a 2023 da kuma tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, wanda kwanan nan ya sauya sheka zuwa jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) daga APC ne ke jagorantar gamayyar.
Sai dai tsohon gwamnan na jihar Ekiti yana ganin hadakar za ta gaza ne saboda gwamnonin jam’iyyar PDP ba sa tare da Atiku, domin suna fafutukar kare kansu a siyasance, kamar yadda ya bayyana acikin shirin siyasa a tashar talabijin ta channels.