Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandare ta Nijeriya (JAMB) ta sanar da ranar 24 ga Afrilu, 2025, a matsayin sabuwar ranar da za a fara zauna jarrabawar ta shekarar 2025 a fadin kasar nan.
Sanarwar ta fito ne daga Fabian Benjamin, mai ba da shawara kan hulda da jama’a na hukumar JAMB ya sanya wa hannu.