A yau ne ake sa ran shugaba Bola Tinubu zai dawo Nijeriya bayan ya shafe kusan makonni biyu a kasar Faransa, kamar yadda mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga ya tabbatar.
A wata sanarwa da Bayo Onanuga ya fitar a Litinin dinnan, ya bayyana cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu zai dawo gida a yau.
Tun da farko dai, fadar shugaban kasar ta bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin cewa shugaban zai ci gaba da gudanar da harkokin mulkin kasar baki daya a kasar Faransa.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis din da ta gabata, Onanuga ya ce, Shugaban ya bar birnin Paris zuwa birnin Landan, ya kuma ci gaba da tattaunawa da manyan jami’an gwamnati, inda yake sa ido kan muhimman al’amuran kasa, ciki har da umarni ga shugabannin tsaro don magance barazanar da ke kunno kai a wasu sassan kasar.