DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnatin jihar Katsina ta kashe Naira bilyan 36.8 kan sha’anin samar da tsaro – Faruq Lawal Jobe

-

Gwamnatin jihar Katsina hadin guiwa da kananan hukumomi 34 na jihar sun kashe kudi Naira bilyan 36.8 wajen samar da tsari mai kyau na inganta tsaron lungu da sako na jihar.

Mataimakin Gwamnan jihar, Faruk Lawal Jobe, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a Katsina, inda ya ce an kashe wadannan kudaden ne tun daga lokacin da gwamnatin Malam Dikko Umaru Radda ta hau karagar mulki a 2023 har zuwa yanzu.

Ya bayyana cewa an yi amfani da kudaden ne wajen sayen motoci masu sulke na (APC) guda 10, motoci samfurin Toyota Hilux guda 65 da kuma babura guda 700.

Haka kuma, ya ce gwamnati ta kashe Naira miliyan 985.9 wajen samar da magani, tallafin kudi da sauran hanyoyin agaji ga wadanda suka samu raunuka ta dalilin ayyukan ta’addanci a jihar.

Mataimakin Gwamnan jihar ta Katsina Faruq Lawal Jobe ya kara da cewa, jimillar mutane 2,286 ne suka amfana da wannan tallafin kudi zuwa yanzu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Kwankwaso ba dan NNPP bane tun 2023, in ji shugaban jam’iyyar na kasa

Shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Dr. Agbo Gilbert Major, ya bayyana cewa Rabi’u Musa Kwankwaso, jagoran tafiyar Kwankwasiyya, ba halastaccen da jam’iyyar ne ba. Yayin da...

Sai kun kara damara wajen yaki da matsalar tsaro – Shugaba Tinubu ya umurci sojojin Nijeriya

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu, ya bukaci jami'an rundunonin tsaron Nijeriya da su kara azama wajen shawo kan kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta. Shugaba Tinubu ya...

Mafi Shahara