Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS za ta yi wa k taro a Ghana a Talatar nan domin tattaunawa kan ficewar kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso.
Taron dai zai gudana a tsawon kwanaki biyu, kamar yadda wata sanarwar kungiyar ta nuna.
ECOWAS ta ce kasashe mambobin kungiyar za su tattauna kan tasirin ficewar kasashen ga hukumomin ECOWAS.
Jaridar PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa a shekarar da ta gabata ne kasashen uku da ke karkashin mulkin soja suka fice daga kungiyar a hukumance.