Hukumar tsaro ta farin kaya ta Nijeriya ta bayar da umarnin tsare wasu jami’an da ake zargin suna da hannu wajen karbar naira miliyan 5.2 daga hannun wani matafiyi, biyo bayan umarnin da ministan harkokin cikin gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo ya bayar.
Umurnin na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun hukumar NSCDC, Afolabi Babawale, a ranar Laraba.
Lamarin wanda ya dauki hankulan jama’a a shafukan sada zumunta, an ruwaito jami’an na karbar kudin ne daga hannun wani matashi da ya taso daga Ado-Ekiti a jihar Ekiti zuwa Akure, jihar Ondo.
A matakin da ya dauka, kwamandan rundunar, Ahmed Audi, ya yi Allah wadai da halayyar da jami’an suka nuna, abin da ya bayyana rashin da’a da kuma saba wa ka’idar aiki da hukumar.