Hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi gargadi game da daukar juna biyu da wuri da ta lura da cewa, hakan yana haddasa mace-macen yara mata masu shekaru 15 zuwa 19 a duniya.
A cikin sabon rahoton da ta fitar, WHO ta bayyana cewa sama da yara mata miliyan 21 ne ke samun juna biyu a kowace shekara a ƙasashe masu karamin karfi, inda kusan rabin waɗannan masu juna biyun basu shirya daukarsa ba.
A cewar hukumar ta lafiya, wannan yana barazana ga inganta kiwon lafiya, yaduwar cututtuka, haihuwar yaran da su da kwarin kashi, da kuma janyo matsaloli a yayin haihuwa.