DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Hisbah a Kano ta rushe wani wurin da ake yada jita-jitar an ga sahun Annabi

-

Hukumar Hisbah a jihar Kano ta rushe wani wuri da ke a Dakata cikin kwaryar birnin, bayan bazuwar jita-jita cewa wurin na dauke da sawun kafa na fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW.

Majiyar DCL Hausa ta jaridar Daily Trust ta ba da labarin cewa, wurin, da a kwana nan aka share domin gina layin dogo, ya ja hankalin dumbin mabiya addinin Musulunci bayan bayyanar wata alamar sawun kafa a cikin laka, tare da fitar ruwa daga wurin.

Jita-jitar da ta yadu cikin gaggawa cewa “Ruwan Albarka” na bubbuga a wurin kuma yana dauke da sawun Annabi, lamarin da ya sa mutane ke zuwa domin neman waraka da samun tubarraki.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Mataimakin Kwamandan Hisbah na jihar Kano, Dr Mujahideen Aminudeen, ya gargadin jama’a da kada su yarda da irin wadannan labaran da ke jefa mutane a hanyar bata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Kwankwaso ba dan NNPP bane tun 2023, in ji shugaban jam’iyyar na kasa

Shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Dr. Agbo Gilbert Major, ya bayyana cewa Rabi’u Musa Kwankwaso, jagoran tafiyar Kwankwasiyya, ba halastaccen da jam’iyyar ne ba. Yayin da...

Sai kun kara damara wajen yaki da matsalar tsaro – Shugaba Tinubu ya umurci sojojin Nijeriya

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu, ya bukaci jami'an rundunonin tsaron Nijeriya da su kara azama wajen shawo kan kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta. Shugaba Tinubu ya...

Mafi Shahara