‘Yan majalisar dokokin jihar Zamfara guda tara da aka dakatar, sun yi wani zaman majalisar dokoki tare da zabar sabon kakakin majalisa, lamarin da ke nuni da ruruwar wutar rikicin siyasar jihar.
‘Yan majalisar, wadanda aka dakatar a watan Fabrairun 2024 bisa zarginsu da rashin da’a, sun yi wani zama na farko a wani wuri da ba a bayyana ba a ranar Laraba, a cewar jaridar Dailytrust.
Yayin zaman sun zabi Hon. Bashir Aliyu Gummi a matsayin shugaba, haka kuma sun umurci Gwamna Dauda Lawal da ya sake gabatar da kudurin kasafin kudin shekarar 2025 a gaban majalisar ta su.
Mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Adamu Aliyu ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, inda ya jaddada bukatar daukar matakin ladabtarwa.