Hukumar zabe mai zaman kanta ta Nijeriya ta bayyana shirin da take yi a bai wa ‘yan kasar da suka cancanta damar kada kuri’a a babban zaben shekarar 2027 ko da kuwa basu da katin zabe na dindindin.
Sai dai hukumar ta ce wannan yunkuri ba zai yi nasara ba har sai majalisar tarayya ta yi gyaran fuska ga dokar zabe.
Babban sakataren yada labarai na shugaban hukumar ta INEC, Rotimi Oyekanmi, ya shaida wa jaridar PUNCH cewa, hukumar ta kudiri aniyar amfani da hanyoyin fasaha domin bai wa ‘yan Nijeriya damar yin zabe.