Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima na jagorantar taron majalisar tattalin arzikin kasa a fadar shugaban Nijeriya, domin tattaunawa kan batutuwa tare da ba shugaban kasa shawara.
Daya daga cikin batutuwan da za su mamaye taron sun hada da matsalar tsaro a wasu sassan kasar nan, musamman jihohin Filato, Benue, Zamfara da Kwara, a cewar jaridar Dailytrust.
Mafi yawan gwamnonin jihohin suka amince da kafa ‘yan sandan jihohi, sai dai har yanzu ba a kai ga cimma matsaya ta karshe ba.